ashfat-aliyu1662135337 Ashfat Aliyu

Wannan littafin sadaukarwa ne ga MBIY Kuma ban yarda wani ko wata ya canja min labari ba duk Wanda yayi hakan Allah ya isa ban yafe ba. Da gaske labarin nan ya faru duk da wani gun n'a canja sa Kuma da dadin wasu abubuwan


Публицистика Всех возростов.
0
1.0k ПРОСМОТРОВ
В процессе - Новая глава Everyday
reading time
AA Поделиться

Tomorrow

Wata ranar Jumma da safiya na fito zagaya gari wata kyakyawan yarinya na gani fara ce ba Can ba dan ta wuce a kirata da wankan tarwada, kyakyawa ce ajin farko, kyakyawan idanunta da zaran ta kalli namiji a duk yanda yake dole ya fada a tarkon kaunar ta, hanci kuwa har baki, a takaice zan ce muku irin Kira coca cola din nan ce watau burin kowane da namiji sai dai muce Mashaallah.

shin wacece wannan yarinya ? Ashley kenan ita din ta kasance ba yar kowa ba, Ashley ta kasance marainiya ce babanta ya rasu sai mamanta sai yayunta biyu Abdoul da Mohamed. Suna rayuwa cikin jin dadi da kaunar junan su tareda maman su duk da dai ita Ashley ta zabi zama a gun kakarsu ta wajen uwa wato Mami kenan jarumar mata ga hakuri iya girki da jajurcewa duk da hakan ya kasance wajibi ne ga duk jinin sarauta basa dauka raini. Takaitacen labarin Ashley kenan.


Cigaban labarin.....

2** Ashley ! Ashley ! naji mama na kiran mafi soyuwa yar tata, "Na'am mama ganin nan zuwa ina saka kaya ne kar nayi late zuwa wajen Mami kin san nace mata yau zan koma" Ammi (maman Ashley kenan) tayi murmuchi 🙂toh ina jiranki. Ba'a wani dauki lokaci mai tsayi ba saiga Ashley ta fito cikin hadaden leshe marron tayi matukar kyau sosai ta fito ta tsaya gaban Ammi taya murmuchi ita ma Ammi murmuchi take wa yar' tata, tace "Ashley ki kula da kanki da mutuncin duk rintsi Kuma ki maida himma ga karatun ki mai hakuri chi keda riba wata rana " murmuchi tayi tace "inshaallah Ammi " a ranta tana dada godewa Allah da samun uwa ta gari kamar Ammi ga hakuri ga tsafta da sannin ya kamata. Hanya ta kama zata fita tace Ammi na tafi harda yar kwalla ta harga Allah tana son mamata bata son abinda zai nisantata da ita a yanzun ma dan ya kasance zata tafi karatu ne tazo ne yin bankwana da mahaifiyarta. Ammi ta chiga rarachinta sai da kyar ta hakura da daina kukan ta Kamo Hanya zuwa gidan Mami................

A can babban birnin kasar ta Niger🇳🇪 watau Niamey kenan ( kasata ni Ashfat marubuciyar littafin Tomorrow na Ashley, ina alfahari da kasantuwa a cikinta 🤗🥰🥰🥰)

Wani kyakyawan saurayi fari dogo na gani kwance a kan tanfatsetsiyar katifarsa yana barci daga gani ko ba'a fada ba barcin gajiya yake yin yanda yake yamutsa fuska abun sai ya ba mutum dariya ma. Fari ne sosai dan sai ka zata ma baya jin hausa idan Kai masa, gachin kansa baki sumul-sumul yacha gyara sai cheki yake yana fitar da kamshi mai dadi, hancin sa har bakinsa sai Pink lips dinsa da ya kama yana cijewa a cikin barci. Abokin sa Adhir ne ya chigo dakin yana cewa "haba mallam soja ka tachi hakan mana mun hada shagali domin ka kai kana nan saï barci kake Ashram ka farka mana" sai a lokacin ne ya iya bude sexy eyes nasa da suka yi masa nauyi domin gajiya ya dubi Abokin nasa baiyi magana ba ya shiga bayi ya sakarwa kansa ruwa.... Wanene Ashram ? Ashram dai haifafen garin Niamey ne , mamar sa bafulatana ce babansa ma ta bangaren tasa mahaifiyar bafulatani ne kakansu Ashram din bahaushe ne ya auri bafulatana, sunan mamar Ashram Djamilat mace mai hakuri sai mijinta Illyass sunada ya'ya shida suna zaune Zaman lafiya da soyayar juna ba mai jin tsakanin, ta hakan ne ta samu damar baiwa yaran Nata tarbiya mai kyau da inganci. Yaran saura suna karatu saura kuwa suna aiki ne, Ashram chine na biyu a ya'yanta yanada yaya Abdoul Razac, saï kaninsa Karim, farid, Shureim, Farida.

A halin yanzu Ashram ya kasance soja ne sous-officiers a nan birnin Niamey bayan karbar horo na musamman a kasar America na tsawon chekara biyu ya komo gida chine Abokin nasa Adhir ya hada masa party murnan dawowar sa. wannan kenan a takaice.

Cigaban labari...

fitowan sa daga wanka direct gaban mirrow ya tsaya yana Kuma caje kansa daga bisani yayi shafe-shafen sa ya bude armoire ya fido kaya suit bakake riga yar ciki fara sai takalma bakake , hum komi black harta glass din dake makale a fuskansa saï kamshi yake zubawa mai narkar da zuciya wani kayatancen murmuchi ya sauke Wanda shi yasan me hakan yake nufi a ransa. Isowa yayi gaban Abokin nasa yace " muje koh?" Kai kurum ya daga domin yasan ba karya abokin nasa ya hadu yanzu ne Yan mata Sun fara yi musu tururuwa , shi kansa Adhir ba baya bane wajen kyau cikar haiba da kyawun fasali. Haka suka jera koda suka dochi wurin Aka dauki shewa party ya Soma wata yar budurwa baka na gani gefin Ashram bazata wuce 22years ba tazo tana jan hannayensa bb muje muyi rawa Halimatu yarinya mai ji da kanta ga naira. Haka suka dau lokaci suna cashe ayarsu, har lokacin Halima tana makale da Ashram so take ta biyosa har dakin sa amma sam Yaki Bata fuska domin Ashram ba irin lalatatun yaran nan bane yanada Yan mata sossai mafi yawancin su kuwa duk suna sonsa ne saboda kyawun sa wasu kuwa hasken fatarsa wasu kuwa dan kakin jikinsa domin suna matukar karbarsa kamar balarabe, hakan ne yasa Yan mata like masa dan ma baya sakar musu fuska.3** Ashley na isa gidan Mami direct dakinta ta wuce tayi chara da wanke-wanke ta dora girki bayan kammalla ta dauki roba ta debi ruwa tachiga bayi tayo wanka, bayan ta fito ta daukibuta domin yin alwala ana cikin yin hakan ne sai ga Mami ta chigo cikin gidan tana mai yin murmuchi 🙂 tace " yar albarka har kin komo " itama murmuchin ta mayar mata tace " eh Mami tun dazu n'a chigo bakya nan ne shiyasa" Mami tace shikenan kije idan kin idar da salar kuzo ina son magana dake dangane da tafiy

2 сентября 2022 г. 18:30:11 0 Отчет Добавить Подписаться
0
Продолжение следует… Новая глава Everyday.

Об авторе

Прокомментируйте

Отправить!
Нет комментариев. Будьте первым!
~